Babu abin da ka tabuka game da cigabanmu – Matasan jihar Sakkwato ga Tambuwal

Babu abin da ka tabuka game da cigabanmu – Matasan jihar Sakkwato ga Tambuwal

Wasu gungun matasa a karkashin inuwar kungiyar daliban jihar Sakkwato sun bayyana gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda bai tabuka komai ba game da cigabaansu, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kungiyar, Isa Usman yana bayyana cewa ya zama wajibi a garesu dasu mara ma jam’iyyar APC baya sakamakon gazawa da gwamnatin jihar Sakkwato ta yi, musamman wajen ciyar da matasan jihar gaba.

KU KARANTA: Osinbajo ya tauna tsakuwa kuma Aya ta ji tsoro: Ministoci 23 sun halarci zaman majalisar zartarwa

Usman yace har yanzu ba a kowani shekara gwamnatin jihar ke biyan daliban jihar tallafin karatu, inda ya kawo misalin barazanar da jami’ar BAZE dake Abuja ya na sallamar daliban jihar Sakkwato dake karatu a jami’ar a dalilin rashin biyan kudin makarantarsu.

Babu abin da ka tabuka game da cigabanmu – Matasan jihar Sakkwato ga Tambuwal

Tambuwal

Shugaba Usman ya tuna yadda ake kulawa da bukatun matasa a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Wammako, inda yace a wancan lokaci babu kakkautawa wajen biyan hakkokin daliban jihar Sakkwato.

Da wannan ne Usman ya bayyana goyon bayan kungiyarsu ga jam’iyyar APC, tare da jaddada mubaya’arsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sanata Aliyu Wammako, daga karshe ya gargadi matasa akan fadawa shaye shaye da dabanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel