Osinbajo ya tauna tsakuwa kuma Aya ta ji tsoro: Ministoci 23 sun halarci zaman majalisar zartarwa

Osinbajo ya tauna tsakuwa kuma Aya ta ji tsoro: Ministoci 23 sun halarci zaman majalisar zartarwa

A wani lamari da ba’a saba ganinsa ba, akalla ministoci ashirin da uku ne suka halarci zaman majalisar zartarwa na gwamnatin tarayya da ake yi a duk ranar Laraba, duk da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a duk lokacin da shugaba Buhari ya yi balaguro zuwa kasashen waje, Ministoci basu cika halartar zaman majalisar zartarwa ba tunda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta, illa kalilan dagfa cikinsu.

KU KARANTA: Inna lillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yar Najeriya ta rasu yayin gudanar da aikin Hajji

Osinbajo ya tauna tsakuwa kuma Aya ta ji tsoro: Ministoci 23 sun halarci zaman majalisar zartarwa

Osinbajo

Sai dai a wannan Larabar, 8 ga watan Agusta, an sha mamaki, inda aka hangi ministoci akalla guda ashirin da uku da suka halarci wannan zama, wanda ake alakanta haka da namijin kokari da mukaddashin shugaba Osinbajo ya yi wajen tsige shugaban hukumar DSS, kuma na hannun daman Buhari, Lawal Daura daga mukaminsa.

Saboda nuna isa ma, Osinbajo bai bari an fara taron da karfe 11 na safe kamar yadda Buhari yake yi ba, sai ya dawo da shi karfe 10 na safiyar yau, kuma duka ministocin sun gama isa fadar shugaban kasa tun karfe 9:30.

Hakazalika an hangi ministocin sun yi gungu gungu suna kus kus a tsakaninsu bayan kammala taron majalisar zartarwar.

Osinbajo ya tauna tsakuwa kuma Aya ta ji tsoro: Ministoci 23 sun halarci zaman majalisar zartarwa

Ministoci

Idan za’a tuna a ranar Talata ne Osinbajo ya yi awon gaba da Lawal Daura daga mukaminsa na shugaban DSS, sakamakon mamaye majalisa da jami’an DSS suka yi ba tare da neman izinin mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ba.

Osinbajo ya tauna tsakuwa kuma Aya ta ji tsoro: Ministoci 23 sun halarci zaman majalisar zartarwa

Ministoci

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel