Yanzu Yanzu: Kotu ta umurci IGP da ya kama shugaban INEC sannan a gabatar da shi a kotu a ranar 14 ga watan Agusta

Yanzu Yanzu: Kotu ta umurci IGP da ya kama shugaban INEC sannan a gabatar da shi a kotu a ranar 14 ga watan Agusta

Justis Stephen Pam na babban kotun tarayya dake Abuja, a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta, ta umurci sufeto janar na yan sanda da ya kama sannan ya gabatar da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta , Mahmood Yakubu, a kotu sakamakon kin bin umurnin kotu.

Justis Pam a ranar 1 ga watan Agusta ta ba da umurnin kama Farfesa Mahood bayan ya ki halartan zaman kotu don nuna dalilin da zai sa baza’a tura sa kurkuku ba akan kin bin umurnin kotu.

Ejike Oguebego da Chuks Okoye, shugaba da maiba jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), shawara a jihar Anambra ne suka shigar da karar.

Yanzu Yanzu: Kotu ta umurci IGP da ya kama shugaban INEC sannan a gabatar da shi a kotu a ranar 14 ga watan Agusta

Yanzu Yanzu: Kotu ta umurci IGP da ya kama shugaban INEC sannan a gabatar da shi a kotu a ranar 14 ga watan Agusta

Mai shari’ar ta sake ba da umurnin kama shugaban hukumar zaben sakamakon kin halartan kotu da yayi duk da umurnin kama shi da aka bayar a ranar 1 ga watan Agusta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan majalisa na PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Kano

Alkalin ta tuna cewa an dage sauraron lamarin zuwa ranar 8 ga watan Agusta domin ci gaba da shari’an na raini da ake tuhumar hukumar INEC da shugabanta, Farfesa Mahmood.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel