Shugaban jam'iyyar PDP, Secondus, ya nemi Shugaba Buhari ya yi murabus

Shugaban jam'iyyar PDP, Secondus, ya nemi Shugaba Buhari ya yi murabus

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ya yi murabus daga kujerar sa sakamakon mamayar da hukumar jami'an tsaro na DSS ta kai majalisar dokoki ta tarayya a ranar Talatar da ta gabata.

Secondus ya bayyana hakan ne da sanadin kakakin sa, Ike Abonyi, inda ya ce aukuwar mamayar ta tabbatar da shugaba Buhari da jam'iyya mai ci ta APC sun daura damarar hallaka dimokuradiyya a kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Secondus ya bayyana cewa an kulla tuggun wannan mamaya ne tare da shugaba Buhari yayin da Sanata Godswill Akpabio ya ziyarce sa a birnin Landan kwanaki kadan da suka gabata.

Shugaban jam'iyyar PDP, Secondus, ya nemi Shugaba Buhari ya yi murabus

Shugaban jam'iyyar PDP, Secondus, ya nemi Shugaba Buhari ya yi murabus
Source: Depositphotos

A sanadiyar haka shugaban jam'iyyar yake kira ga al'ummar Najeriya da kuma na kasashen ketare dangane da yadda gwamnatin Buhari ke yiwa 'yan Majalisa da shari'a karan tsaye da kuma cuzgunawa abokanan adawa da lamarin ya zamto tamkar mulkin kama karya.

KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata 'yan takara na jam'iyyar APC

Da wannan ne shugaban jam'iyyar yake kira shugaba Buhari akan ya yi gaggawar murabus domin al'ummar kasar su samu dama ta ci gaba da sharbar romon dimokuradiyya.

Secondus ya kuma yabawa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, dangane da gaggawar tsige shugaban hukumar ta DSS da ta aiwatar da mamaya a majalisar dokoki ta tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel