Inna lillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yar Najeriya ta rasu yayin gudanar da aikin Hajji

Inna lillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yar Najeriya ta rasu yayin gudanar da aikin Hajji

Hukumar kula da jin dadin alhazan Najeriya, NAHCON, ta sanar da mutuwar guda cikin Alhazawan Najeriya, wata Hajiya dake gudanar da aikin Hajji a kasar Saudiyya, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban tawagar likitocin dake kulawa da mahajjatan Najeriya a kasar Saudi, Ibrahim Kana ne ya tabbatar da mutuwar Hjaiyar a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta, inda yace Matar ta fito ne daga jihar Kano.

KU KARANTA: Bahallatsar mamaye majalisa: Shugaban PDP ya roki Birtaniya ta dukunkuno Buhari zuwa Najeriya

Inna lillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yar Najeriya ta rasu yayin gudanar da aikin Hajji

Mahajjata

“A ranar Talata wata daga cikin Alhazawan Najeriya ta rasu, wanda dama tana samun kulawa a wajenmu sakamakon ciwon siga dake damunta, daga baya sai ciwon yayi kamari, daga bisani muka garzaya da ita zuwa babban Asibitin Sarki Abdul Aziz, inda ta rasu a can.” Inji shi.

Rahotanni sun tabbatar da Hajiyar yar asalin karamar hukumar Ungogo ce na jihar Kano, sai dai ba bayyana sunanta ba, sakamakon har yanzu ba’a sanar da yan uwanta ba. Da fatan Allah ya gafarta mata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel