Hukumar EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Benue a bankuna 3

Hukumar EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Benue a bankuna 3

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta daskarar da asusun gwamnatin jihar Benue a bankuna uku.

Babban sakataren labarai na gwamnan jihar, Mista Terver Akase, ya tabbatar da hakan ga majiyarmu ta Chennels Television a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta.

Akase yayi Allah wadai da abunda hukumar ta EFCC tayi, cewa Gwamna Samuel Ortom zai yi Magana akan lamarin a yau a Abuja, babban birnin tarayya.

Hukumar EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Benue a bankuna 3

Hukumar EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Benue a bankuna 3

An tattaro cewa daskarar da asusun da hukumar yaki da cin hanci da rashawa tayi ya kasance saboda bincike da ake yi akan zargin almubazaranci da kudin tsaron jihar Benue.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan majalisa na PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Kano

Don haka gwamnatin jihar tayi zargin cewa hakan na daga cikin makircin da ake kullawa gwamnan jihar saboda barin APC da yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel