Yanzu Yanzu: Yan majalisa na PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Kano

Yanzu Yanzu: Yan majalisa na PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Kano

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi babban asara na wasu manyan mambobinta guda shida a majalisar dokokin jihar Kano inda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan majalisar da suka sauya sheka sune masu wakiltan kananan hukumomin Gwarzo, Gwale, Gezawa, Rogo, Madobi da Bichi na jihar Kano.

Yanzu Yanzu: Yan majalisa na PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Kano

Yanzu Yanzu: Yan majalisa na PDP 6 sun sauya sheka zuwa APC a Kano

A halin yanzu, gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta ta bayyana sauya shekar mataimakin gwamna, Farfesa Hafiz Abubakar daga jam’iyyar All Progressive Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin tsohon labari.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon Sanata Dino Melaye ya na saida gyada a kai ya jawo magana

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya tsige wasu kwamishinonin sa biyu da suka tarbi Sanata Godswill Akpabio tare da lale maraba yayin da ya sauka a filin jirgin sama dake babban birnin jihar na Uyo.

Kwamishinonin da suka debo ruwan dafa kansu sun hadar da; Victor Anatai na ma'aikatar al'adu da yawan buda idanu da kuma Ibanga Akpabio, na ma'aikatar kwadago wanda ya kasance dan uwa ga sanatan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel