ASUU ta fara maganar yajin aiki bayan an kasa cin ma matsaya da Gwamnatin Tarayya

ASUU ta fara maganar yajin aiki bayan an kasa cin ma matsaya da Gwamnatin Tarayya

Bisa dukkan alamu dai abubuwan ba su tafiya daidai tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya watau ASUU bayan da Kungiyar tayi barazanar za tayi watsi da wani shirin sulhu da ake yi da Gwamnatin kasar.

ASUU ta fara maganar yajin aiki bayan an kasa cin ma matsaya da Gwamnatin Taryya

Gwamnatin Tarayya da ASUU sun gagara cin ma daidaito

Malaman Jami’a na kasar ba su yi amanna da Dr. Wale Babalakin da aka nada a matsayin Shugaban kwamitin da Gwamnati ta shirya su zauna da Kungiyar ASUU ba. An nada kwamiti ne domin a duba yarjejeniyar da aka yi a 2009.

A jiya Talata ASUU ta tabbatar da cewa zaman da ake yi da kwamitin Wale Babalakin ya rushe saboda kwamitin na nunawa Malaman Jami’o’i na Najeriya taurin-kai. ASUU tace kwamitin da aka kafa bai da niyyar cin ma matsaya.

KU KARANTA: Ba za mu yarda a taba Saraki ba Inji su Kwankwaso

ASUU ta fadawa Ministan ilmi na kasa Adamu Adamu cewa su na iya shiga wani sabon yajin aikin idan har aka gaza yin sulhu tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya. Shugaban Kungiyar na kasa Biodun Ogunyemi ya bayyana wannan.

Tun a farkon 2017 ne Buhari ya kafa wani kwamiti na Gwamnati da za ta zauna da Kungiyar ASUU domin magance sabanin da ake samu a da. An shirya kammala zaman ne cikin’yan kwanaki amma har yau ba a cin ma matsaya ba.

Bayan wani taro da aka yi kwanan nan a Garin Kalaba, Kungiyar ASUU tace tabbas Dr. Wale Babalakin bai da shirin ganin an yi sulhu. ASUU ta zargi Kwamitin Babalakin da kokarin nunawa Malaman makarantun kasar ba su iya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel