Mark, Jang, Kwankwaso da wasu Sanatoci 46 dake goyon bayan Saraki

Mark, Jang, Kwankwaso da wasu Sanatoci 46 dake goyon bayan Saraki

Mun samu rahoton cewa akwai jerin Sanatoci 49 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar dakatar da duk wani yunkuri na tsige shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki daga kujerar sa tare da mataimakin sa, Ike Ekweremadu.

Wannan lamari ya biyo bayan mamayar da hukumar DSS ta kai ga Majalisar dokoki ta tarayya a da hakan ya sanya mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tsige shugaban ta a ranar Talatar da gabata.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta jaridar The Punch da Daily post suka ruwaito, an gabatar da wannan sunaye a mashiga ta Majalisar dokoki ta tarayya da mafi rinjayen sa ya kunshi Sanatoci na jam'iyyar adawa ta PDP.

Jerin Sanatocin da sanadin shafin jaridar Daily Post

Jerin Sanatocin da sanadin shafin jaridar Daily Post

Jerin Sanatocin da sanadin shafin jaridar Daily Post

Jerin Sanatocin da sanadin shafin jaridar Daily Post

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, Sanata Jonah Jang da kuma Sanata Abiodun Olujimi na cikin jerin Sanatocin da ke fafutikar dakile duk wani yunkuri na tsige Saraki tare da Mataimakin sa daga mukaman su.

KARANTA KUMA: Gwamna Emmanuel ya tsige Kwamishinonin sa 2 da suka yi lale maraba ta Sanata Akpabio

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne wata kungiya ta Sanatocin jam'iyyar APC suka gudanar da zaman su cikin farfajiyar majalisar dattawa domin dakatar da ci gaba da hutun majalisar da ta shiga tun makonni biyu da suka gabata.

Babbar manufar gudanar da wannan zama bai wuci fara gabatar da shirye-shiryen tsige shugaban majalisar dattawa da kuma mataimakin sa, inda sanatocin jam'iyyar PDP suka yi gaggawar warware shirin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel