Jam’iyyar APC tayi Allah wadai da mamayar da aka kai majalisar dokokin kasar

Jam’iyyar APC tayi Allah wadai da mamayar da aka kai majalisar dokokin kasar

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) tayi Allah wadai da mamayar da jami’an yan sandan farin kaya wato DSS suka kai majalisar dokokin kasar sannan ta nisanta kanta daga lamarin.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta saki ta hannun mukaddashin shugaban labaranta, Yekini Nabena tace ita mai bin doka ce.

Jam’iyyar APC tayi Allah wadai da mamayar da aka kai majalisar dokokin kasar

Jam’iyyar APC tayi Allah wadai da mamayar da aka kai majalisar dokokin kasar

“Jam’iyyarmu ta nisanta kanta daga duk wani farmaki da hari da zai yi barazana ga damokradiyyar kasarmu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin Najeriya sun yi Allah wadai da mamayar da aka kai majalisar dokokin kasar

“Jam’iyyarmu mai bin doka cesannan kuma tana shawartsan dukkanin yankuna das u kasance masu bin kundin tsarin mulkinmu da damokradiyarmu."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar gwamnonin Najeriya sun yi Allah wadai da mamayar da jami’an hukumar yan sandan farin kaya wato DSS suka kai majalisar dokokin kasar a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Shugaban kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari, a wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 8 ga watan Agusta ya yi kira ga a hukunta dukkanin wadanda ke da hannu akan mamayar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel