Wata Ma’aikata ta karkatar da Biliyan 1.3 wajen aikin bogi a Najeriya

Wata Ma’aikata ta karkatar da Biliyan 1.3 wajen aikin bogi a Najeriya

- Wasu Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya sun karkatar da Biliyoyin kudi a 2016

- Bincike ya nuna cewa OORBDA ta batar da wasu Biliyoyi wajen ayyukan bogi

Bincike ya nuna yadda wasu Ma’aikatu ke karkatar da kudi a Gwamnatin Buhari

Wasu Ma’aikatun Tarayya su na karkatar da kudin Gwamnati

Mun samu labarin yadda wata Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya ta barnatar da mahaukatan kudi wajen wasu ayyuka na bogi. Jaridar Premium Times ta kasar nan cewa tayi wannan bincike.

Ma’aikatar OORBDA mai kula da ruwan da ya tashi da Jihar Ogun zuwa Osun ta kashe sama da Naira Biliyan 1.3 a 2016 ba tare da bin ka’ida ba. Wani rahoto da Odita Janar na kasar nan ya fitar ya tabbatar mana da wannan.

KU KARANTA: Hotunan Fadar Shugaban kasar Najeriya masu ban kaye

Manyan Jami’an Hukumar ta OORBDA sun kashe makudan kudi wajen wasu ayyuka da aka gaza yin su da kyau a lokacin da kuma aka yi watsi da wasu ayyukan da ya kamata. Hakan dai ya sabawa ka’ida da tsarin aiki na kasar.

Manyan Ma’ikatan Hukumar dai sun karkatar da kudin Gwamnati ne wajen ayyukan bogi da coge. Binciken ya nuna cewa an saki kudin wasu kwangilolin da ba ayi da kyau ba domi kurum su samu hanyar lamushe kudin Gwamnati.

KU KARANTA: Osinbajo zai hukunta masu laifi a Najeriya

A baya dai ofishin Odita-Janar na kasar nan ya fitar da wani rahoto inda ya nuna cewa akwai wasu Biliyan 28 da aka karkatar bayan an ware su da nufin maganin matsalolin kawararowar hamada da zaizayar kasa a wasu Jihohin kasar.

Dama a makon nan kun ji yadda PDP ta lissafo wasu manya-manyan satan da aka tafka a Gwamnatin APC cikin shekara 3. Jam’iyyar adawar tace yaudarar mutanen gida da waje ake yi da sunan yaki da sata a Gwamnatin Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel