Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata 'yan takara na jam'iyyar APC

Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata 'yan takara na jam'iyyar APC

Aisha Buhari, Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta sha alwashi gami da tabbatar da goyon bayan mata ma su sha'awar neman takara karkashin inuwa ta jam'iyyar APC, domin a dama da su cikin harkokin siyasa a kasar nan.

Uwargidan ta shugaban kasa ta bayar da wannan tabbaci ne a ranar Talatar da ta gabata, yayin zababbiyar shugabar Mata ta kasa ta jam'iyyar APC tare da shugabannin jam'iyyar na kowace jiha na kasar nan suka ziyarce ta a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya na Abuja.

Kungiyoyin da suka ziyarce ta sun hadar da shugabannin mata na yankin Arewa ta tsakiya, Arewa ta Gabas, Arewa ta Yamma, Kudu ta Gabas, Kudu ta Yamma da kuma na Kudancin Kudu, inda shugabar mata ta kasa ta jam'iyyar APC, Mrs Salamatu Baiwa ta jagorance su.

Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata 'yan takara na jam'iyyar APC

Aisha Buhari ta sha alwashin goyon bayan Mata 'yan takara na jam'iyyar APC

Hajiya Aisha take cewa, Mata a kasar nan sun bayar da muhimmiyar gudunmuwa tare da taka rawar gani wajen nasarar da zabubbukan da suka gudana cikin kasar nan ta Najeriya a shekarun baya.

Ta ci gaba da cewa, lokaci ya karato da ya kamata a fara damawa da Mata cikin harkokin siyasa tun daga tushe inda kuma ta neme su akan tsayuwar daka wajen da'a ga kundin tsari na jam'iyyar su.

KARANTA KUMA: Osinbajo na sake ganawa da Sufeto Janar na 'Yan sanda

Ta kuma yi kira ga Matan akan su ci gaba da goyon bayan gwamnatin jam'iyyar APC wajen ciyar da kasar nan zuwa ga gaci tare da neman fitowa kwansu da kwarkwata wajen damawa cikin harkokin siyasa.

A na ta jawaban, Hajiya Salamatu ta bayar da tabbacin ta ga uwar gidan shugaban kasa wajen hada kan mata tare da goyon bayan su wajen yi ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel