2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe

2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe

Kungiyar magoya bayan shugaban kasa Buhari reshen arewa ta tsakiya, a ranar Talata, 7 ga watan Agusta sun kaddamar da cewa baby wani shugaban Najeriya a yanzu haka da zai iya kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa kungiyar wacce ke gangamin sake zabar shugaba Buhari tayi Magana a taron manema labarai a Abuja domin bayyana manufar ayyukan kungiyar.

Shugaban kungiyar, Williams Ozi-Raji, yace martaba da nasarorin shugaban kasar zasu yi masa Magana a zaben 2019.

2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe

2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe

A cewar Ozi-Raji, an kammala shirye-shirye domin kaddamar da tsare-tsaren ayyukan cigaba a fadin jihohin arewa maso tsakiya akan bukatar sake zabar shugaban kasar karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: Ban bar APC saboda dalilai na son zuciya ba – Gwamna Ahmed

Kungiyar tayi ikirarin cewa shugaba Buhari ya magance cin hanci da rashawa, da rashin adalci cewa hakan yayi nasarar daidaita tattalin arzikin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel