Ban bar APC saboda dalilai na son zuciya ba – Gwamna Ahmed

Ban bar APC saboda dalilai na son zuciya ba – Gwamna Ahmed

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, yayi bayanin cewa sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki abune da ginshikan jam’iyyar suka haddasa.

Vanguard ta rahoto cewa Abdulfatah ya bayyana hakan a Ilorin lokacin da ya karbi bakuncin jami’an kungiyar Oro Descendants Union (ODU) karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Uthman Balogun, wadda ya kai masa ziyarar bangirma a gidan gwamnati.

Ahmed ya fadama bakinsa cewa ya bar jam’iyyar APC lokacin da ya zamana cewa ana nuna wariya da zalunci ga mutanen jihar da suka taimaka 100 bisa 100 wajen zabarsa.

Ban bar APC saboda dalilai na son zuciya ba – Gwamna Ahmed

Ban bar APC saboda dalilai na son zuciya ba – Gwamna Ahmed

A cewarsa, duk kokari da akayi don tabbatar da cewa an mutunta mutanen jihar Kwara da yi masu adalci ya ci tura saboda wadanda ke jam’iyyar sun kasance masu son zuciyarsu ta hanyar nuna wariya ga sauran masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Emmanuel ya tsige Kwamishinonin sa 2 da suka yi lale maraba ta Sanata Akpabio

Ahmed yace duk fafutukar da yake yi saboda mutanen jihar Kwara ne da suka taimaka matuka wajen cigaban Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel