Jami’an DSS sun yi farin ciki da korar Lawal Daura daga aiki

Jami’an DSS sun yi farin ciki da korar Lawal Daura daga aiki

Mun samu labari cewa Jami’an Hukumar tsaro ta DSS masu fararen kaya sun yi farin ciki da jin labarin cewa Mukaddashin Shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki jiya.

Jami’an DSS sun yi farin ciki da korar Lawal Daura daga aiki

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kori Shugaban DSS

Majiyar mu ta bayyana mana cewa an barke da murna da shewa a sa’ilin da labari ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ke rike da kasar na rikon kwarya ya kori Shugaban Hukumar DSS Lawal Daura daga ofis.

Har a Hedikwatar DSS wanda ake kira Yello House, Ma’aikata sun yi farin cikin jin cewa an sallami Shugaban na su daga aiki. A 2015 ne Shugaba Buhari ya dawo da Lawal Daura ofis ya rike DSS bayan an yi masa ritaya a baya.

KU KARANTA: Farfesa Yemi Osinbajo ya sake ganawa da Shugaban 'Yan Sanda

Rahota ya kuma zo mana cewa Jami’an tsaron da aka aika su tare Majalisar kasar jiya ma sun ji dadin jin labarin cewa Lawal Daura ya bar ofis. An dai soki abin ya auku jiya a Majalisar kasar wanda yayi sanadiyyar korar Daura daga aiki.

A halin yanzu Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo ya nada Matthew Seiyefa a matsayin wanda zai rike ofishin Shugaban DSS kafin a nada sabon Shugaba bayan an sallami Lawal Daura. Har Osinbajo ya gana da Seiyefa jiya a ofishin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel