Dirar mikiyar da jami’an tsaro suka yi ne ya yiwa taron da muka yi niyya katsalandan – Saraki da Dogara

Dirar mikiyar da jami’an tsaro suka yi ne ya yiwa taron da muka yi niyya katsalandan – Saraki da Dogara

- Sa toka sa katsin majilisa da jami'an tsaro a jiya, Saraki da Dogara sun yi magana

- Shugabannin majalisun kasar nan sun fitar da jawabin nasu ne a wata takarda dake dauke da sa hannunsu

- Biyo bayan mamayar da jami'an DSS din suka kai ne har ta kai ga an sauke shugaban hukumar daga mukaminsa a jiya

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara sun bayyana cewa rashin zaman majalisar da bai samu ba a jiya ya ta'allaka ne akan yadda jami'an rundunar tsaro ta farin kaya suka yiwa majalisar tsinke, tare da hana mambobin majalisar shiga zauren majalisar domin tattaunawa.

Dirar mikiyar da jami’an tsaro suka yi ne ya yiwa taron da mu kayi niyya katsalandan – Saraki da Dogara

Dirar mikiyar da jami’an tsaro suka yi ne ya yiwa taron da mu kayi niyya katsalandan – Saraki da Dogara

Tun da farko dai shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ya kirawo zaman majalisar na gaggawar domin sake yin nazari akan kasafin kudin da hukumar zabe ta kasa wato INEC ta bukata, kamar yadda shugaba Muhammad Buhari ya bukace su da su zauna.

KU KARANTA: 2019: Bamu da wadda ya kai Buhari wajen sanyin hali – Kungiyar yakin zabe

Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da Saraki and Dogaran suka fitar, ta bayyana cewa ba su samu damar zaman majalisar ba sakamakon hana su shiga da jami'an rundunar tsaro ta farin kaya suka yi.

Sanarwar ta kara da cewa jami'an rundunar tsaron farin kaya sun yiwa farfajiyar majalisar tsinke tare da hana mambobin majalisar shiga, har ta kai ga keta mutuncin akawun majalisar Alhaji Mohammed Sani Omolori.

Bugu da kari, shugabannin Majalisun sun bayyana cewa cincirondan jami'an tsaro a farfajiyar majalisar tare da cin zarafin mambobinta baya kan tsarin demokaradiyya.

A karshe sanarwar ta bayyana cewa jiya Talata ta zama wata bakar rana ga dimukuradiyyar kasar nan.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel