APC na kokarin nada Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa - Sanata Bruce

APC na kokarin nada Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa - Sanata Bruce

Labari ya zo mana cewa Jam’iyyar APC mai mulki na kokarin nada Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya. Sanata Ben Murray Bruce ne ya bayyana wannan a jiya da safe.

APC na kokarin nada Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa - Sanata Bruce

Sanata Ben Murray Bruce ya nemi irin su Ingila su takawa APC burki

Sanatan da ke wakiltar wani Yanki na Jihar Bayelsa a Majalisar Dattawa Ben Murray Bruce yace Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan ta shirya tsaf da yunkurin tsige Bukola Saraki daga matsayin san a Shugaban Majalisar Najeriya.

Fitaccen ‘Dan Majalisa yake cewa ana kokarin nada Sanatan Akwa Ibom na Arewa maso Yamma ne ya haye kujeran na Bukola Saraki. Sanata Ben Bruce ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan ne lokacin da aka samu takaddama a Majalisar.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar nada Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Sanatan na Jam’iyyar PDP yace APC ta shirya tsige har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan watau Ike Ekweremadu. Sanata Bruce ya kuma ce APC ba za ta iya tsige Saraki ba domin kuwa ba su da yawan da za su iya yin hakan.

Murray Bruce ya kuma bayyana cewa su na magana da kasashen waje domin ganin Gwamnatin Tarayya ba tayi wa harkokin Majalisa shiga sharo ba shanu ba. Sanatan yace aiko Jami’an DSS da aka yi cikin Majalisa ya sabawa dokar kasa.

Dama kun san cewa wani Sanata ya bayyana cewa da zarar an dawo hutun da Majalisa ta tafi za a tsige Bukola Saraki wanda ya koma PDP, ba mamaki a maye gurbin na sa da Sanata Godswill Akpabio wanda shi kuma ke neman shigowa APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel