Bahallatsar mamaye majalisa: Shugaban PDP ya roki Birtaniya ta dukunkuno Buhari zuwa Najeriya

Bahallatsar mamaye majalisa: Shugaban PDP ya roki Birtaniya ta dukunkuno Buhari zuwa Najeriya

Shugaban jam’iyyar PDP, Cif Uche Secondus ya yi tir da mamaye majalisar dokokin Najeriya da jami’an hukumar DSS suka yi a ranar Talata, 7 ga watan Agusta da nufin hana yan majalisu gudanar da aikinsu yadda ya kamta, inji rahoton Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Uche yana kira ga gwamnatin kasar Birtaniya da ta gaggauta dukunkuno shugaban kasa Muhammadu Buhari dake hutu a birnin Landan, tare da fatattakarsa ya dawo Najeriya, sakamakon zarginsa da yake yi da hannu cikin mamaye majalisar.

KU KARANTA: Mamaye majalisa: Sanatan Jam’iyyar PDP ya wanke Lawal Daura da soso da sabulu

Shugaban PDP ya zargi Buhari da hannun cikin bahallatsar da ta faru a majalisar, inda yace Buhari ya boye a kasar Birtaniya, amma yana cin dunduniyar Dimukradiyya a Najeriya, don haka yayi kira da gwamnatin kasar da ta bai kamata su bari ana amfani da kasarsu wajen shuka tsiya ba.

Bahallatsar mamaye majalisa: Shugaban PDP ra roki Birtaniya dukunkuno Buhari zuwa Najeriya

Jami'an DSS

“An kammala shirya afka ma majalisar ne a yayin da Sanata Godswill Akpabio ya ziyarci Buhari a birnin Landan ne, kuma muna sane da cewa gwamnatin nan bata da suran wani abin da zata tabuka, amma duk abinda za ta yi muna dai dai da ita.” Inji shi.

Daga karshe Uche ya jinjina ma mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo bisa matakin da ya dauka na sallamar shugaban hukumar DSS, Lawal Daura a jiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel