Tattalin Arziki: Danyen mai ya sake hawa bayan Amurka ta sanya wa iran takunkumi

Tattalin Arziki: Danyen mai ya sake hawa bayan Amurka ta sanya wa iran takunkumi

- Kasar Chana da US suna fada akan cinikayya

- Fadan ne ya jawo tashin gwauron zabi da kudin mai yayi

- Kasar Chana nata kokarin ganin kudin kasar ta bai fadi warwas ba

Tattalin Arziki: Danyen mai ya sake hawa bayan Amurka ta sanya wa iran takunkumi

Tattalin Arziki: Danyen mai ya sake hawa bayan Amurka ta sanya wa iran takunkumi

Fadan cinikayya tsakanin kasar chana da US da yaki ci, yaki cinyewa na daya daga cikin abinda ke kawo hauhawa a farashin mai.

Kasar Chana dai na kokarin ganin darajar kudin kasar ta bai fadi ba.

Danyen mai na Brent ya kai dala 73.62. Na US kuma ya kai dala 68.82 a duk ganga daya.

Danyen man Brent yakamata ya kai dala 100. A cikin ranakun karshen mako ne kasar Chana ta canza salon kasuwancin ta tsakanin kasashe, inda ta kara tsadar da zata hana kudin ta lalacewa.

Wannan ya taimaka gurin janye faduwar Yuan na watanni 14. Ya kuma kara wa dalar Australia daraja.

Kudin Australiya ya daga inda ya kai 0.7412 na dala bayan a da yana 0.7403 na dala.

A rana juma'a ne Dow ya hau zuwa kashi 0.54 cikin dari, sai S&P 500 ya samu ribar kashi 0.46 a cikin dari kuma Nasdaq ta karu da kashi 0.12 cikin dari.

Hakan ya faru ne ta hanyar hadin guiwa mai karfi, duk da dai sune cike da zullumin Fadan kasuwanci.

DUBA WANNAN: 'Akpabio ne zai zama shugaban majalisar dattijai'

Fadan kasuwancin dai har yanzu shine babban zance a kasuwancin kasar Chana inda suke bukatar kayan kimanin dala biliyan 60 a ranar juma'a.

Shugaba Donald Trump kuwa yace hanyoyin da yake bi don ganin ya rage kudin da kasar Chana zata dinga amsa na shigar da kaya kasar su ya wuce tunanin mai tunani. Zai kawo faduwa ga kasuwancin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel