Biyayya ta ga Kwankwaso ya janyo ma ni cin kashi a jihar Kano - Hafiz Abubakar

Biyayya ta ga Kwankwaso ya janyo ma ni cin kashi a jihar Kano - Hafiz Abubakar

A ranar Talatar da ta gabata ne tsohon Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya bayyana gamsassun dalilan sa dangane da cin kashi da ya fuskanta a karkashin gwamnatin jihar.

Tsohon mataimakin gwamnan ya yi watsi da ikirarin gwamnatin jihar na cewar an biya sa kimanin Naira Miliyan 120 a wani lokaci yayin da yake kan kujerar sa ta Mataimakin gwamna.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Farfesan ya bayyana fushin sa karara yayin ganawa da manema labarai dangane da ikirarin gwamnatin jihar da a cewar sa kazafi ne gami da shaci fadi.

Yake cewa, ya fuskanci cin kashi daga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje a sakamakon biyayya da yake yiwa ubangidan sa a faggen siyasa, Sanata Rabi'u Kwankwaso.

Biyayya ta ga Kwankwaso ya janyo ma ni cin kashi a jihar Kano - Hafiz Abubakar

Biyayya ta ga Kwankwaso ya janyo ma ni cin kashi a jihar Kano - Hafiz Abubakar

A cewar sa, dukkanin ikiraran kakakin gwamnatin jihar ta Kano, Mallam Muhammad Garba, ba su wuci karairayi gami da shaci fadi da kagaggun zantuka domin kawo nakasu ga amincin sa da kuma shafa masa baki fenti a idanun duniya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta gargadi 'yan takarar Gwamna 11 akan kai hari ga 'Yan adawa

A sanadiyar haka tsohon mataimakin gwamnan jihar ya kalubalanci gwamna Ganduje tare da makarraban sa akan su gabatar da gamsassun shaidu domin kafa hujja akan ikiraran su.

Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon gwamnan ya yi murabus ne daga kujerar sa a sanadiyar wannan cin kashi da ya rika fuskanta daga gwamnatin jihar kuma ya sauta sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel