14 daga cikin ‘yan majalisar dokokin wata jihar kudu zasu tsallaka zuwa APC

14 daga cikin ‘yan majalisar dokokin wata jihar kudu zasu tsallaka zuwa APC

Jita-jita tayi karfi a kan cewar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom zasu canja sheka zuwa APC daga PDP bayan komar tsohon gwamnan jihar, Godswill Akpabio, zuwa jam’iyyar.

Wata majiya daga cikin majalisar dokokin jihar ta Akwa Ibom ta shaidawa jaridar Vanguard cewar mambobin majalisar 14 na shirin komawa APC a ranar Laraba yayin bikin dawowar Akpabio jam’iyyar da za a yi a filin wasa na garin Ikot Ekpene.

Ko a jiya, Litinin, saida shugaban majalisar dokokin jihar, Mista Onofiok Luke, ya jagoranci 24 daga cikin mambobin majalisar 26, suka ziyarci gwamnan jihar, Mista Udom Emmanuel, domin jaddada goyon bayansu gare shi. Sai dai majiyar ta Vanguard ta bayyana wannan ziyara a matsayin siyasa kawai.

14 daga cikin ‘yan majalisar dokokin wata jihar kudu zasu tsallaka zuwa APC

Gwamna Udom Emmanuel da 'yan majalisar dokokin jihar Akwa Ibom

Daga cikin ‘yan majalisar 14 da ake saka ran zasu bi Akpabio akwai NSE Ntuen, dan majalisar dake wakiltar mazabar da Akpabio ya fito, Essien Udim.

A wani labarin na Legit.ng kun karanta cewar a yau ne tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Godswill Akpabio, ya samu tarba daga jami’an gwamnati, ‘yan majalisar dokoki da dubban jama’a yayin da ya ziyarci jihar a yau, Talata.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da tsige Lawal Daura ne saboda yana taimakon Saraki

Wannan it ace ziyara ta farko da Akpabio ya kai jihar sat a Akwa Ibom bayan ya canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A ranar Lahadi ne Akpabio ya ziyarci shugaba Buhari a kasar Ingila inda suka tattauna gabanin komawarsa jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel