Mamaye majalisa: Sanatan Jam’iyyar PDP ya wanke Lawal Daura da soso da sabulu

Mamaye majalisa: Sanatan Jam’iyyar PDP ya wanke Lawal Daura da soso da sabulu

Guda cikin Sanatocin jam’iyyar PDP, da suka sha gwagwarmaya da jami’an hukumar DSS da suka mamaye majalisar dokokokin Najeriya a ranar Talata, 7 ga watan Agusta, Sanata Ben Murray Bruce ya wanke tsohon shugaban shugaban hukumar DSS, Lawal Daura.

Bruce ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da yan jaridu a farfajiyar majalisar, inda yace gwamnati na neman wanda zata daura ma laifi ne kawai sai ta huce fushinta akan shugaban DSS, ta hanyar tsige shi daga mukaminsa.

KU KARANTA: Tsige shugaban DSS: Saura babban sufetan Yansandan Najeriya – Inji APC Tawariyya

“Ban taba ganin juyin mulki mara ma’ana ba irin wannan, wadanda suka shirya juyin mulkin ma basu iya ba, don haka ina fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbata ya hukunta duk masu hannu cikin wannan juyin mulki don kuwa basu iya ba.

Mamaye majalisa: Sanatan Jam’iyyar PDP ta wanke Lawal Daura da soso da sabulu

Bruce da Lawal

“Kaga babu ruwan Lawal Daura a wannan bahallatsa, ni na san yan siyasa ne ke fada masa abinda zai yi, suna neman wanda zasu huce akansa ne kawai, don na ji jam’iyyar APC na cewa bata da masaniya game da mamaye majalisarmu da jami’an tsaro suka yi.” Inji shi.

Daga karshe Sanata Bruce ya bayyana jin dadinsa da yadda gwamnatin Najeriya ke kokarin wanke kanta daga wannan bahallatsa, da kuma yadda jam’iyyar APC ke musanta hannu cikin lamarin, don haka yace sun ji kunya, amma yace a shirye suke idan har Sanatocin APC zasu sake shirya wata makarkashiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel