Tsige shugaban DSS: Saura babban sufetan Yansandan Najeriya – Inji APC Tawariyya

Tsige shugaban DSS: Saura babban sufetan Yansandan Najeriya – Inji APC Tawariyya

Tun bayan tsige shugaban hukumar tsaro ta sirri, DSS, Lawal Daura da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi, yan Najeriya na ta tofa albarkacin bakunansu game da lamarin, wanda babu wanda yi tsammanin faruwar hakan.

Su ma kungiyar APC Tawariyya a karkashin jagorancin Buba Galadima ba’a barta a bay aba, inda aka jiyota a ranar Talata, 7 ga watan Agusta tana jinjina ma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinba kan wannan namijin kokari da ya yi.

KU KARANTA:

Sai dai APC Tawariyya tace ba’a nan take ba, tunda dai ba duka shuwagabannin hukumomin tsaron dake da hannu cikin mamaye majalisar aka ladabtar ba, inda ta nemi Osinbajo da ya tsige babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris Kpotun.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin APC Tawariyya, Kasim Afegbua ne ya bayyana haka a madadin jam’iyyar, inda ya bayyana mamaye majalisa da jami’an DSS suka yi a matsayin wata makarkashiya na kokarin tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki daga mukaminsa.

Afegbua yace wannan lamari ya bar tabo a siyasar Najeriya,: “Tun yaushe muka lalace haka, inda zalunci da mugunta ya yi mana katutu? Muna kuka da wannan salon mulki na shugaban kasa Muhammadu Buhari, mun jin zafin irin siyasar bindigan da ya bullo da shi

“Mun yi tir da yadda jami’an tsaro ke shiga al’amuran siyasa, mun yi Allah wadai da yadda APC ta dage lallai sai ta tsige Sanata Saraki, daga yanzu sunan APC ya koma hadakar jam’iyyar yan juyin mulki.” Inji shi.

Daga karshe Afegbua ya bayyana cewa dukkan alamu sun nuna hukumar DSS ta zamto wani bangare ne na jam’iyyar APC, don haka yayi kira da yan Najeriya su tashi tsaye wajen kare Dimukradiyya, tare da tabbatar da matsayin Najeriya ta Giwar Afrika.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel