An sallami 'Dalibai 33 bisa laifin satar amsa daga jami'ar Bayero ta jihar Kano

An sallami 'Dalibai 33 bisa laifin satar amsa daga jami'ar Bayero ta jihar Kano

Kamar yadda rahotanni da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, hukumomin jami'ar Bayero ta jihar Kano, ta sallami dalibai 33 sakamakon aikata laifukan satar amsa ta jarrabawar da ta gudanar a kakar 2017/2018.

Shugaba mai kula da harkokin gudanar da jarrabawa ta jami'ar, Hajiya Amina Abdullahi, ita ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin din da ta gabata.

Hajiya Amina take cewa, hukumar jami'ar ta bayar da amincewar ta ne dangane da wannan hukunci bayan taron ta karo na 365 da ta gudanar.

An sallami 'Dalibai 33 bisa laifin satar amsa daga jami'ar Bayero ta jihar Kano

An sallami 'Dalibai 33 bisa laifin satar amsa daga jami'ar Bayero ta jihar Kano

Ta ci gaba da cewa, akwai kuma dalibai 12 da jami'ar za ta tursasa su maimaita shekara guda yayin da ja kunnen wasu 70 tare da daga idanun ta na gira.

KARANTA KUMA: Kujerar Shugaban 'Kasa: Dankwambo na neman goyon bayan wakilan PDP a Arewa maso Yammacin Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, jami'ar ta yanke wannan hukunci ne bisa tanadin sashe 19.17 na dokokin jarrabawa kamar yadda Hajiya Amina ta bayyana.

A shekarar da ta gabata ne jami'ar ta sallami wasu dalibai 44 bisa aikata makamancin wannan miyagun laifuka na satar amsa yayin gudanar da jarrabawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel