Kalli yadda aka yiwa Saraki bayan ya shiga majalisa (bidiyo)

Kalli yadda aka yiwa Saraki bayan ya shiga majalisa (bidiyo)

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya samu kyakyawar tarba majalisar dokoki bayan ya kai ziyara majalisa biyo bayan mamayar da DSS suka kai.

Vanguard ta ruwaito cewa Saraki ya isa majalisa da yammacin ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

Sanatoci da mambobin majalisar wakilai na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sunyi wakar nasara da biyayya a yayinda Saraki ya iso majalisar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hadakar jami’an tsaron hukumar ‘yan sanda da na SARS sun kama shugaban hukumar tsaro ta DSS, Lawal Daura, da Osinbajo ya sallama daga aiki yau dinnnan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Osinbajo na ganawar sirri da Magu, da sabon mukaddashin shugaban DSS

An kama Daura ne bisa zarginsa da katsalandan a zaman lafiyar kasa. Yanzu haka yana tsare a shelkwatar SARS ta kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel