INEC ta gano wasu boyayyun tashoshin zabe a masallatai da coci a Najeriya

INEC ta gano wasu boyayyun tashoshin zabe a masallatai da coci a Najeriya

Hukumar zabe na kasa watau INEC ta bayyana cewa ta gano tashoshin zabe har 19 da ba a san da zaman su ba a Jihar Akwa-Ibom. Kwamishinan zaben da ke Yankin, Mike Igini ya tabbatar da wannan.

INEC ta gano wasu boyayyun tashoshin zabe a masallatai da coci a Najeriya

Hukumar INEC ta gano cuwa-cuwar zaben da wasu su ka shirya

Mike Igini wanda shi ne babban Jami’in INEC da ke Jihar Akwa-Ibom a Ranar Litinin ya bayyana cewa sun gano wasu wuraren zabe da Hukuma ba ta san da zaman su ba a Garuruwan Obot Akara da kuma Uyo da ke cikin Jihar ta Kudu.

Kwamishinan zaben watau REC ya bayyana wannan ne wajen wani taron masu ruwa-da-tsaki na zabe mai zuwa. Igini yace an bude wuraren zabe kusa da masallatai da coci da kuma otel da yanzu Hukumar ta INEC za ta gyarawa zama.

KU KARANTA: Gwamnan Adamawa ya canza Kwamishonin da su ka koma PDP

Inda aka shirya ajiye akwatunan zaben ya sabawa ka’idojin Hukumar INEC kuma babu mamaki ‘Yan siyasa ne su ka kintsa wannan aiki domin murde zaben badi. Hukumar zaben tace yanzu babu wanda ya isa yayi murdiya a kasar.

Hukumar dillacin labarai na kasar nan watau NAN ta rahoto cewa Hukumar zaben ta canzawa wasu wuraren zaben wuri inda ta kuma tabbatarwa jama’a cewa za ayi zabe mai nagarta a shekara mai zuwa wanda ba za a kare a Kotu ba.

INEC wanda nauyin gudanar da zabe ya rataya a kan ta a Najeriya ta kirkiro wata sabuwar fasahar zamani da za ta sa a kawo karshen magudi. Wannan fasaha zai yi maganin satar kayan zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel