Da dumin sa: Jam'iyyar hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta rabe gida 2

Da dumin sa: Jam'iyyar hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta rabe gida 2

Kimanin kasa da watanni uku kacal da hada gamayyar jam'iyyun hadakar nan da suka sha alwashin fatattakar shugaba Buhari a zaben 2019 karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Obasanjo ta African Democratic Congress (ADC) ta rabe gida biyu.

Wannan dai ta bayyana ne a kunnuwan jama'a biyo bayan taron manema labarai da shugaban yan aware na sabuwar jam'iyyar da yayiwa lakani da New African Democratic Congress (N-ADC) mai suna Cif Precious Elekima ya kira a garin Abuja.

Da dumin sa: Jam'iyyar hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta rabe gida 2

Da dumin sa: Jam'iyyar hadakar fatattakar Buhari ta Obasanjo ta rabe gida 2

KU KARANTA: Muhimman batutuwa 5 da ya kamata ku sani game da Lawal Daura

Legit.ng ta samu cewa Cif Precious Elekima ya ce sun yanke shawarar raba jam'iyyar ne saboda sun gano wasu na cin dunduniyar su a sabuwar tafiyar ta hanyar yin gaban kansu ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.

A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar nan ta masoya shugaba Buhari da kuma Osinbajo watau Buhari/Osinbajo Again (BOA) a turance na kasa baki daya mai suna Alhaji Yahya Hammajulde yayi murabus daga mukamin sa sannan kuma ya fice daga jam'iyyar sa ta APC.

Ita dai kungiyar Buhari/Osinbajo Again (BOA) kamar yadda muka samu, kungiya ce da ke da karfin gaske a yankin Arewa maso gabashin kasar nan da aka kafa domin kare muradu da kuma yiwa Buhari kamfe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel