Yanzu Yanzu: An cinna wa kayyayakin sakatariyar APC wuta a Delta

Yanzu Yanzu: An cinna wa kayyayakin sakatariyar APC wuta a Delta

Rikicin da ke tunkarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, a jhar Delta ya sauya salo a ranar Talata, 8 ga watan Agusta yayinda fusatattun mambobin jam’iyyar suka cinna wa kayyayakin sakatariyar karamar hukumar Isoko South wuta.

Koda dai ba’a bayyana abubuwan dake kewaye da lamarn ba a loacin wannan rahoto, majiyoyi sun bayyana cewa baida alaka da hadewar jami’an jam’iyyar a yankin.

Wata majiya a yankin wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa a jiya ne aka rantsar da shugabannin kananan hukumomin jam’iyyar na Oleh sashi na 1 da 2.

“A yau wasu fusatattun mambobin jam’iyyar sun fasa sakatariyar, suka cire dukkanin kujeru,teura da sauran kayyayakin ofis, suka fito dasu waje sannan suka kona su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki ya isa zauren majalisar dokoki

“Jam’iyyar tayi kokarin hade jamianta saboda a samu zaman lafiya a jam’iyyar, sai dai wadannan mutane basu ji dadin yadda aka tafiyar da tsarin ba saboda suna ganin an ware su”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel