Tsige shugaban hukumar DSS: Wani Gwamna daga yankin Arewa ya bayyana farin cikinsa

Tsige shugaban hukumar DSS: Wani Gwamna daga yankin Arewa ya bayyana farin cikinsa

Gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ya bayyana farin cikinsa tare da jinjina ma mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo bisa matakin daya dauka akan shugaban hukumar tsaro ta sirri, DSS, Lawal Daura.

A ranar Talata, 7 ga watan Agusta ne Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki, sakamakon mamaye majalisar dokokin Najeriya da jami’an hukumar DSS suka yi, inda suka hana Sanatoci daga shiga majalisar.

KU KARANTA: Zan hukunta duk wadanda suka shirya ma Majalisa manakisa – Inji Mukaddashin shugaban kasa

Wannan ne ya sanya Osinbajo jin ta bakin shugaban DSS, amma bai sami wani gamsashshen bayani ba, hakanan hukumar ta yi gabanta kanta ne a wannan aiki ba tare da neman izinin mukaddashin shugaban kasa, hakan ya sa ba tare da bata lokaci ba Osinbajo ya tsige Daura daga mukaminsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan jihar Benuwe, Ortom yana yaba ma Osinbajo, inda yace matakin da ya dauka ya yi daidai, inda yace yan Najeriya sun dade suna tsimayin ganin an tsige Lawal Daura duba da yadda yake tafiyar da hukumar DSS.

Daga bisani gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta duba sauran hukumomin tsaron Najeriya don fatattakan baragurbi marasa kishin kasa daga cikinta, don tabbatar da ingancin tsaron Najeriya, da jama’an kasar gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel