Yanzu Yanzu: Saraki ya isa zauren majalisar dokoki

Yanzu Yanzu: Saraki ya isa zauren majalisar dokoki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya isa majalisar dokokin kasar.

Saraki da hadimansa sun iso majalisar dokokin ne jim kadan bayan hukumar DSS ta sauke takunkumin da ta sawa bangaren dokoki.

Shigarsa harabar majalisar yasa magoya bayansa suka fara gaishe shi da taken ‘Baba Oloye’.

Yanzu Yanzu: Saraki ya isa zauren majalisar dokoki

Yanzu Yanzu: Saraki ya isa zauren majalisar dokoki

Ya gaisa da sanatoci da mambobin majalisar wakilai dake cike da farin ciki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An janye jami’an tsaro daga majalisar dokokin kasar

Ana sanya ran cewa shugaban majalisar dattawan zai yi jawabi ga kasa a ranar Laraba aan abubuwan da suka faru a majalisa a kwanakin nan.

Za’a gudanar da tattaunawar ne a majalisa da misalin 12 na rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel