‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane 7 a Borno

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane 7 a Borno

- Har yanzu da ragowar burbushin 'yan tada kayar baya a arewa maso gabashin kasar nan

- Duk da ikirarin rundunar Sojojin kasar nan na kakkabe su, 'yan Boko Haram din sun lababu sun sake tafka barna

‘Yan Boko Haram haye kan motaci da babura sun kai hari wani kauye mai suna Munduri wanda yake kilomita takwas da arewancin Maiduguri, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi inji wani mazaunin kauyen mai suna Abdullahi Bunu.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane 7 a Borno

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane 7 a Borno

‘Yan ta’addan sun kame mutane bakwai sannan suka bankawa kauyen wuta, kamar yadda shugaban ‘yan kato da gora na kauyen Umar Ari ya shaidawa jami'an tsaro ta wayar tarho.

"Yau da safen nan mun dawo kawai sai muka tarar an kone kauyen kurmus har da kayan abincinmu da komai namu".

A kwanakin baya ‘yan tada kayar bayan suka kai hare-hare domin cigaba da yada aikidarsu inda suka kai hari a sansanin Sojin kasar nan, wanda ake zargin wasu jami’an Sojojin sun rasa rayukansu.

KU KARANTA: Kowa ya sai rariya: Sojoji sun damke wasu gayu 2 masu ci da guminsu

Rahotanni sun tabbatar cewa kungiyar ta Boko Haram ta rabu gida biyu, sai dai ba za’a iya gane su wane daga ciki suka kawo harin ba. Akwai bangaren Abubakar Shekau wanda suka yi fice wajen kaiwa mutane da garuruwa hari, sai kuma bangaren Abu Mus'ab Albarnawi wanda suke ikirarin kai hari ga jami'an tsaro.

A satin da ya gabata ma sai da ‘yan tada kayar bayan suka kashe mutane biyar a yankin Garsawa dake Monguno.

Wannann rikici na yan tada kayar baya ya dauki tsawon shekaru tara kenan ana yinsa, inda ‘yan tada kayar bayan suke ikirarin zasu kafa daular musulunci, wanda aka yi kiyasin sun kashe mutane sama da dubu 20 tare da raba mutane daga gidajensu da garuruwansu, sama da miliyan 2.6.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel