Ra’ayoyin yan Najeriya game da tsige shugaban hukumar DSS da Osinbajo ya yi

Ra’ayoyin yan Najeriya game da tsige shugaban hukumar DSS da Osinbajo ya yi

Ra’ayoyi mabambanta sun bayyana daga bakunan yan Najeriya daban daban game da matakin tsigewa da mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya dauka akan shugaban hukumar DSS, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Idan za’a tuna, da safiyar ranar Talata, 7 ga watan Agusta ne jami’an DSS suka tare kofar shiga majalisar dokokin Najeriya, inda suka hana wasu Sanatocin jam’iyyar PDP shiga farfajiyar majalisar, duk da cewa majalisar na hutu, har sai watan Satumba za’a bude ta.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Mukaddashin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar DSS

Ra’ayoyin yan Najeriya game da tsige shugaban hukumar DSS da Osinbajo ya yi

Osinbajo da Lawal

Sai daga daga bisani bayan yan majalisun sun matsa, jami’an sun bude musu hanya, wannan tataburza da aka sha tsakanin Sanatoci da Jami’an DSS ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa na cewa wai Sanatocin APC zasu tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Majiyar Legit.ng ta jiyo wani dan Najeriya mai suna Francis Ihedioha yana cewa Buhari zai warware wannan hukunci na Osinbajo idan ya dawo, shi kuwa Sefiyunmi Adensay cewa yayi sallamar ba kawai ta ta’allaka ga tare kofatr majalisa bane, dama ya dade yana yin shirme, wanda kuma hakan ya shafi bangaren zartawa, sun dade suna hakuri da shi.

Kemisola Adekunle tace Osinbajoa ya yi, dan kishin kasa ne, yayin da Williams Abba yayi zargin Buhari na da hannu a sallamar Daura, kawai dai ya bari ne sai bayan ya fita, Isamaila Sadiq ya jinjin ma Osinbajo a matsayinsa na jarumi mara tsaro mai hikima.

Daga karshe Muhsin Must Excel ya yi maraba da matakin da Osinbajo ya dauka, inda yace ba abu bane mai sauki daukan matakin da ya dace a mawuyacin hali, ita kuma Enike tace “Me zai sa ba zai zama shugaban kasan ba gaba daya?”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel