Sai da na roki ‘yan majalisar Kano don kada su tsige mataimaki na, amma ya watsa min kasa a ido

Sai da na roki ‘yan majalisar Kano don kada su tsige mataimaki na, amma ya watsa min kasa a ido

- Magangu na cigaba da fito tun bayan ajiye mukamin da mataimakin gwamna da Farfesa Hafiz Abubakar yayi a Kano

- Inda gwamnan Kano Ganduje ya bayyana irin rawar da ya taka don ganin ya ceto mataimakin nasa daga tsigewa amma daga karshe yayi murabus

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa shi ne ya roki ‘yan majalisar jihar kada su tube tsohon mataimakin gwamnan.

Sai da na roki ‘yan majalisar Kano don kada su tsige mataimaki na, amma ya watsa min kasa a ido

Sai da na roki ‘yan majalisar Kano don kada su tsige mataimaki na, amma ya watsa min kasa a ido

Hakan ya fito ne a cikin wata takarda da gwamnan ya aikewa da tsohon mataimakin nasa.

Tsohon mataimakin gwamnan Farfesa Hafiz Abubakar dai ya bayyana cewa ya ajiye mukamin nasa ne saboda rashin fahimta da suke samu a tsakaninsa da gwamnan.

Sai dai Gandujen ya musanta zargin da ake na rashin martaba ofishin mataimakin gwamnan.

KU KARANTA: Mutane 5 da zasu iya maye gurbin kujerar mataimakin gwamnan Kano

Gwamnan ya ce "Idan zaka iya tunawa ni ne wanda na hana ‘yan majalisa tsige ka duk da cewar sun sanya hannu wajen ganin an cireka daga ofishinka".

Gwamnan ya kara da cewa duk da Faefesan ya ajiye mukamin nasa yana masa fatan alheri da kuma girmama hukuncin nasa da ya dauka.

Dama dai Hafiz Abubakar magoyin bayan Kwankwanso ne wanda shi ma suka dauki tsawon lokaci suna dauki ba dadi da gwamna mai ci.

A shekara ta 2014 ne Kwankwanso ya dauko Hafiz Abubakar daga Jami'ar Bayero dake Kano ya kawo shi cikin siyasa a matsayin wanda zai yiwa Gandujen mataimaki.

Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun bayyana cewa akwai mutane guda biyar da kowannensu yake kokarin ganin ya maye gurbin da Hafiz din ya bari.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel