Da duminsa: An kama Lawal Daura an tsare shi bayan Osinbajo ya kore shi daga aiki

Da duminsa: An kama Lawal Daura an tsare shi bayan Osinbajo ya kore shi daga aiki

Labarin da jaridar Legit.ng ta samu ya tabbatar mata da cewar hadakar jami’an tsaron hukumar ‘yan sanda da na SARS sun kama shugaban hukumar tsaro ta DSS, Lawal Daura, da Osinbajo ya sallama daga aiki yau dinnnan.

An kama Daura ne bisa zarginsa da katsalandan a zaman lafiyar kasa.

Yanzu haka yana tsare a shelkwatar SARS ta kasa.

Idan baku manta ba jaridar Legit.ng ta kawo maku rahoton da dumi-duminsa cewar mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tsige shugaban hukumar tsaro ta farin kaya da aka fi sani da DSS, Malam Lawal Daura, daga mukaminsa biyo bayan farmakin da jami’an hukumar sa suka kai majalisar dokokin Najeriya da safiyar ranar Talata 7 ga watan Agusta.

Da duminsa: An kama Lawal Daura an tsare shi bayan Osinbajo ya kore shi daga aiki

Lawal Daura

Legit.ng ta wallafa cewar kakakin mataimakin shugaban kasa Osinbajo, Laolu Akande ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 7 ga watan Agusta.

DUBA WANNAN: An bawa Sanatocin APC dalar Amurka miliyan $1m domin su tsige Saraki

Kazalika hadimin shugaban kasa Buhari akan harkokin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya tabbatar da fatattakar Lawal Daura daga aiki.

Bugu da kari, Farfesa Osinbajo ya umarci Lawal Daura ya mika ragamar tafiyar da hukumar ga jami’I mafi girma a hukumar, har sai baba ta ji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel