Afkawa Majalisa: Osinbajo ya yi tattaunawar sirri da shuwagabannin hukumomin tsaro

Afkawa Majalisa: Osinbajo ya yi tattaunawar sirri da shuwagabannin hukumomin tsaro

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shuwagabannin manyan hukumomin tsaro guda biyu, da suka hada da Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris da shugaban hukumar tsaro ta sirri, DSS, Lawal Daura.

Legit.ng ta ruwaito wannan tattaunawa tsakanin Osinbajo, Idris da Daura baya rasa nasaba da farmakin da jami’an hukumar DSS suka kai ma Majalisar dokokin kasar da safiyar Talata, 7 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Mukaddashin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar DSS

Afkawa Majalisa: Osinbajo ya yi tattaunawar sirri da shuwagabannin hukumomin tsaro

Osinbajo

Sufetan Yansandan ne ya fara isa fadar shugaban kasa don amsa kiran mukaddashin shugaban kasa yayin da Lawal Daura ya isa fadar bayan misalin mintoci goma sha biyar.

Idan za’a tuna, da safiyar yau ne jami’an DSS suka tare kofar shiga majalisar dokokin Najeriya, inda suka hana wasu Sanatocin jam’iyyar PDP shiga farfajiyar majalisar, duk da cewa majalisar na hutu, har sai watan Satumba za’a bude ta.

Sai daga daga bisani bayan yan majalisun sun matsa, jami’an sun bude musu hanya, wannan tataburza da aka sha tsakanin Sanatoci da Jami’an DSS ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa na cewa wai Sanatocin APC zasu tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel