'In qura ta lafa, Akpabio ne zai zamo shugaban majalisar dattawa'

'In qura ta lafa, Akpabio ne zai zamo shugaban majalisar dattawa'

- An tura jami'an DSS sun rufe majalisar kasar nan a yau da safe

- Shugabann kasa ya sauke shugaban DSS din kan hakan

- Kokarin sauke Saraki ne duk ya jawo yamutsin

'In qura ta lafa, Akpabio ne zai zamo shugaban majalisar dattawa'

'In qura ta lafa, Akpabio ne zai zamo shugaban majalisar dattawa'

A kokarin jaam'iyyar APC na tsige na uku a kasar nan, an ga jami'an yansandan farin kaya na sirri watau SSS dauke da muggan makamai suna shawagi a majalisar kasa don hana 'yan majalisar kasar shiga suyi aikinsu.

A kan haka ne ma, jama'ar kasar nan suka dauki zafi inda suka dinga kwatanta rigimar da kutse irin na zamanin mulkin soja.

Sai dai a martanin gwamnatin Buhari, an sauke shugaban DSS din daga mukaminsa domin wai ya zaqe da nuna bangaranci a siyasa.

DUBA WANNAN: Amurka ta sanya wa Iran karin takunkumai

Shi kuwa dan adawa daga PDP, Ben Murray Bruce, Sanata daga Bayelsa, cewa yayi, idan qura ta laa Najeriya su shirya ganin tsohon gwamnan Akwa Ibom Akpabiyo, wanda ya sauka daga mukaminsa na shugaban marasa rinjaye, a matsayin na uku a kasar nan.

Idan Akpabio da gaske ya zama na uku a kasar nan, wannan na nufin an gyaro ta kenan ta karkashin kasa don shugaba Buhari ya sami goyon bayan wasu daga Neja Delta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel