Yanzu Yanzu: Sanatoci 49 sun nuna adawa da yunkurin tsige Saraki da Ekweremadu

Yanzu Yanzu: Sanatoci 49 sun nuna adawa da yunkurin tsige Saraki da Ekweremadu

Akalla sanatoci 49 na tarayyar Najeriya ne suka nuna adawarsu da yunkurin tsige shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Farfesa Ike Ekweremadu.

Ku tuna cewa tun a asubahin yau ne jami’an DSS suka mamaye majalisar dokokin Najeriya sannan suka hana mutane shiga harabar majalisar.

Haka zalika jami’an tsaron sun hana yan majalisa da dama, musamman masu biyayya ga Saraki da Ekweremadu shiga majalisar yayinda suka bar yan APC suka shiga.

Yanzu Yanzu: Sanatoci 49 sun nuna adawa da yunkurin tsige Saraki da Ekweremadu

Yanzu Yanzu: Sanatoci 49 sun nuna adawa da yunkurin tsige Saraki da Ekweremadu

Sanatan dake wakiltan Bayelsa ta gabas Ben Murray-Bruce yayinda ya jagoranci sauran yan majalisa wajen adawa da mamayar, yace sanatocin APC ne suka shirya hakan sannan kuma cewa suna shirin tsige Saraki da Ekweremadu sannan su daura sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA KUMA: APC ba zata iya nasara a zaben 2019 ba – Inji Lamido

Yace wannan makirci da sanatocin APC ke shiryawa ba zai yi nasara ba domin jam’iyyar PDP ce ke da masu rinjaye a majalisar dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel