Cin mutuncin da gwamnatin tsakiya keyi wa dimokuradiyya ya fara kufular da 'yan Najeriya

Cin mutuncin da gwamnatin tsakiya keyi wa dimokuradiyya ya fara kufular da 'yan Najeriya

- Gabatowar zaben 2019 yasa gwamnatin tarayya ta takurawa wa 'yan adawa

- Tashin hankali ya kunno kai a satin da ya gabata inda yan sanda da jami'an hukumar yaki da rashawa suka bayyana a gidajen Bukola Saraki da Ike Ekweremadu

- 'Yan sanda sun taimakawa wani bangare na majalisar jihar Benue a yunkurin tsige Gwamna Samuel Ortom

Cin mutuncin da gwamnatin tsakiya keyi wa dimokuradiyya ya fara kufular da 'yan Najeriya

Cin mutuncin da gwamnatin tsakiya keyi wa dimokuradiyya ya fara kufular da 'yan Najeriya

Tunkarowar zaben 2019 ne yasa gwamnatin tarayya ta takurawa yan adawa inda take amfani da jami'an tsaro gurin bata yanayin siyasar kasar.

A satin da ya gabata ne jami'an yan sanda da na hukumar yaki da rashawa suka tsinkayi gidajen Bukola Saraki da Ike Ekweremadu, shugaban majalisar dattawa da mataimakin shi da sanyin safiya.

Saraki ya tsallake tarkon in da ya samu shiga majalisar tare da jagorantar sanatoci 14 na APC zuwa jam'iyyar PDP da African Democratic Party. Amma Ekweremadu bai samu damar tsallake tarkon ba.

Makamancin hakan ya faru a majalisar wakilai, inda mahukuntan 37 suka canza sheka.

DUBA WANNAN: Asarar jama'a zuwa ga talauci a Najeriya

Wannan mummunar dabi'a na faruwa ne a duk shekaru 4,lokacin da zabe ya gabato. Burin cigaba da zama a kan kujerun ke jawo hakan.

Sati daya da ya gabata, yan sanda sun rufe majalisar jihar Benue, amma kuma Gwamna Ortom ya canza sheka da ga APC zuwa PDP.

A zabubbukan da suka gabata, yan Najeriya sun dandana irin wannan izaya da jam'iyya mai mulki ke gasa musu, wanda akan hakan ne Buhari yayi kamfen din kawo canji amma sai gashi a yanzu ma bata canza zani ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel