Kalli bidiyon wata budurwa da ta lakadawa wani kwastoma da yaki biyanta kudinta

Kalli bidiyon wata budurwa da ta lakadawa wani kwastoma da yaki biyanta kudinta

- Wata mata ta ci zarafin wani saurayi don ya hana ta kudin giyar da ya sha

- Bidiyon ya nuna yadda ta rika kutufarsa tana tambayar ta bata kudinta

- Shi kuma cikin maye sai sambatu yake

Yanzu haka dai wani bidiyo na tashe inda yake ta zagaya shafukan sada zumunta a kasar Kenya, bidiyon wanda ya ke nuna yadda wata matashiyar budurwa take dukan wani matashi da yake cikin mayen giya bisa kin biyanta kudin giyar da ya sha kimanin Dala 2.

Wannan al'amari ya jawo hankalin al'ummar kasar tare da haifar da maganganu daga bangarorin jama'a da dama.

Kalli bidiyon wata budurwa da ta lakadawa wani kwastoma da yaki biyanta kudinta

Kalli bidiyon wata budurwa da ta lakadawa wani kwastoma da yaki biyanta kudinta

Cikin bidiyon an nuna budurwar tana marin saurayin gami da tattaka shi tare da tambayar lalla-lallai ya bata kudinta. Mutumin yana cikin mayen giya wanda hakan ya sanya suturar jikinsa ta ke kokarin cirewa.

KU KARANTA: Wani matashi ya zartar da hukuncin Zina akan wasu abokansa guda 2

Al'amari dai ya jawo hankalin mahukuntan kasar ta Kenya wanda har ta kai babban Daraktan sauraron kararraki na kasar Noordin Haji ya bukaci dukkanin wanda yake da cikakken bayanin al'amarin da ya gabato gabansu domin sanar da su don su zurfafa bincike

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel