To fa! Shugaban kasa ya tsige wani Minista a Ghana

To fa! Shugaban kasa ya tsige wani Minista a Ghana

- Guguwar tsige-tsige da sauya sheka ba a iya Najeriya kadai ta tsaya ba

- Har ta leka Kasar Ghana, inda a can ma Shugaban kasar ya tsige wani Ministansa

Wani bayani da ya fito daga fadar shugaban kasar Ghana ya tabbatar da umartar ministan filaye da ma`adinan kasar Boakye Agyarko day a mika mukamin nasa ga John Peter Amewu kafin ayi sabon nadi.

To fa! Shugaban kasa ya tsige wani Minista

To fa! Shugaban kasa ya tsige wani Minista

Sallamar Ministan makamashin za ta fara aiki ne nan take kamar yadda 'yar gajeriyar sanarwa ta bayyana wadda ke dauke da rattaba hannun daraktan sadarwa na fadar shugaban kasar Mista Eugene Arhin.

KU KARANTA: Tsige Saraki: An bawa Sanatocin APC miliyan $1m

Duk da yake babu wani dalili da aka bayar na sallamar Ministan daga aiki, amma masu sharhi na zargin hakan ba ya rasa nasaba da yarjejeniyar makamashi ta AMERI da kasar ta shiga tun lokacin tsohuwar gwamnatin NDC, wadda jam`iyya mai mulki ta NPP ta yi ta suka tare da shan alwashin soke ta da zarar ta hau mulki.

Ministan makamashin ya fara shan matsin lamba ne tun bayan da ya yi ikirarin yunkurin sake sabunta yarjejeniyar ta AMERI, kan hujjar cewa ta fi wacce aka kulla a baya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Shugaban kasar ta Ghana Akufo-Addo ya nada Minista Agyarko ne tun a shekarar 2017 da ta gabata.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel