Yanzu Yanzu: An hana magatakardan majalisar dokokin kasar shiga majalisa

Yanzu Yanzu: An hana magatakardan majalisar dokokin kasar shiga majalisa

Yayinda ake ci gaba da yiwa majalisar dokokin kasar kawanya, an hana magatakardan majalisar dokokin kasar, Alhaji Mohammed Sani Omolori, shiga majalisar.

Oolori ya isa zangon majalisar dokokin da misalin karfe 10:02 na safe, amma jami’an DSS da suka yiwa waje kawanya sun hana shi shiga majalisar.

A yayinda magatakardan ya isa majalisar dokokin, ya tunkari jami’an DSS din kan dalilin da yasa aka haa ma’aikatansa da sauran mutane shiga harabar.

Yanzu Yanzu: An hana magatakardan majalisar dokokin kasar shiga majalisa

Yanzu Yanzu: An hana magatakardan majalisar dokokin kasar shiga majalisa

Sai suka maida masa da martanin cewa suna yin yadda aka umurce su ne daga sama.

Sai ya juya cikin fushi ya bar wajen amma yayi jawabi ga ma’aikatan majalisar dokokin inda ya bukaci su kwantar da hankalinsu kamar yadda bai san mai ke faruwa ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye harabar majalisar dokokin kasar (bidiyo)

Ya kuma gargade su da kada su dauki doka a hannunsu, inda ya tabbatar masu da cewa baya da hannu cikin abunda ke faruwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel