Buhari ne zai lashe zaben 2019 – Inji Jibrin

Buhari ne zai lashe zaben 2019 – Inji Jibrin

Dan majalisa mai wakiltan mazabar Bebeji/Kiru a majalisar wakilai, Dr Abdulmumin Jibrin, ya yarda cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake nasara a zaben 2019.

Jibrin wadda ya kasance bako a gidan talbijin din Channels Television yace yayi imani sauya shekar wasu shugabannin jam’iyyar Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) ba zai hana shugaban kasar yin nasara a zabe ba.

Sai dai dan majalisar ya yarda cewa zaben zai yi zafi sosai.

Buhari ne zai lashe zaben 2019 – Inji Jibrin

Buhari ne zai lashe zaben 2019 – Inji Jibrin

Ya bayyana cewa tsatsauran zabe shine mafi kyau ga kasar damokradiya, yayinda nasarar zai karfafa masu adawa, ya kuma kara ingancin kowani mambobin jama’a sannan kuma jam’iyya mai mulki ba zata yi sanya ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsohon magatakardan APC, Abdullahi ya zama kakakin jam’iyyar CUPP

Ya kuma bayyana wasu abubuwan da suka sanya shi yarda cewa Buhari zai lashe zabe, kamar fannin tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel