Yanzu-yanzu: Sanatoci magoya baya Buhari suna ganawar gaggawa a Otel

Yanzu-yanzu: Sanatoci magoya baya Buhari suna ganawar gaggawa a Otel

Sanatoci magoya bayan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, sun bayyana cewa abokan aikinsu magya bayan shugaba Muhammadu Buhari na ganawa a wani Otel dake cikin birnin tarayya Abuja domin tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Daga cikin sanatocin, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa suna can a yanzu domin shirye-shiryen aiwatar da aiki.

Sanata Dino Melaye yace: " Sanatoci magoya bayan gwamnati a yanzu suna gana a Sheraton Hotel inda zasu kaddamar da tsiga."

An fara rikicin tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ne tun lokacin da ya alanta sauya shekarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC), zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA: Yan kunar bakin wake 5 sun hallaka a harin da suka kai Maiduguri

Wasu yan majalisan jam'iyyar APC a jawaban kusa-kusa sun yi gargadi cewa ba za'a samu zaman lafiya a majalisa ba sai an tsige Saraki.

Da safen nan, NAIJ. ta kawo muku rahoton cewa jami'an hukumar DSS sun yiwa majalisar zobe inda suka hana yan majalisun PDP shiga.

Daga baya wasu daga cikinsu sun samu shiga bayan rikice-rikice. Daga cikin sanatocin da suka samu shiga sune Rafiu Ibrahim, Shaba Lafiagi, Isa Hamma Misau, Ben Murray Bruce, Biodun Olujimi, Nazif Gamawa, Atai Aidoko, Ahmed Ogembe, Chukwuka Utazi, da sauransu.

Babu dan majalisan APC da aka gani a majalisan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel