Yanzu Yanzu: Tsohon kakakin APC, Abdullahi ya zama kakakin jam’iyyar CUPP

Yanzu Yanzu: Tsohon kakakin APC, Abdullahi ya zama kakakin jam’iyyar CUPP

Jam’iyyar hadin gwiwa mai kokarin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2019 mai zuwa ta nada tsohon babban sakataren jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mallam Bolaji Abdullahi, a matsayin kakakinta.

An sanar da Abdullahi wadda yayi murabus daga matsayinsa na kakakin jam’iyya mai mulki a matsayin shugaban kwamitin labarai na sabuwar jam’iyyar hadin gwiwar, wanda a ciki harda Kazeem Afegbua da Kola Ologbondiyan.

Yanzu Yanzu: Tsohon magatakardan APC, Abdullahi ya zama kakakin jam’iyyar CUPP

Yanzu Yanzu: Tsohon magatakardan APC, Abdullahi ya zama kakakin jam’iyyar CUPP

Kwamitin Abdullahi na daga cikin kwamitocin da jam’iyyar CUPP ta kaddamar a jiya a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye harabar majalisar dokokin kasar (bidiyo)

Jam’iyyar CUPP jam’iyya ceda ta hada jam’iyyu 38 ciki harda babban jam’iyyar adawar kasar wato Peoples Democratic Party (PDP) domin fitar da dantakara guda daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel