Yadda Gwamnatin Tarayya ke amfani da Kuɗaɗen da Abacha ya sace

Yadda Gwamnatin Tarayya ke amfani da Kuɗaɗen da Abacha ya sace

Za ku ji cewa an yi walƙiya domin kuwa gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske dangane da yanayi na kashe kuɗaɗen da aka dawowa ƙasar nan, wanda tsohon shugaban ƙasa na Mulkin soji, Marigayi Janar Sani Abacha ya wawura cikin asusun gwamnati.

Ministan labarai da al'adu na ƙasa, Alhaji Lai Muhammad, shine yayi wannan ƙarin haske yayin ganawa da manema labarai cikin babban birnin ƙasar nan na tarayya a ranar Litinin din da ta gabata.

Alhaji Lai Muhammad yake cewa, gwamnatin tarayya ta na amfani da kuɗaɗen ne wajen harkokin tsarin nan na tallafawa gami da bayar da hannun jari sabanin yadda mafi akasarin mutane a ƙasar suka dauka na cewar ana raba wannan kuɗaɗe ne ga talakawa da gajiyayyu.

Ministan yake cewa, ko kusa bai kamata al'ummar kasar nan su yi tunanin ana rabe wannan kuɗaɗe ga talakawa bayan da gwamnatin kasar Switzerland ta dawowa da Najeriya dukiyar ta.

Yadda Gwamnatin Tarayya ke amfani da Kuɗaɗen da Abacha ya sace

Yadda Gwamnatin Tarayya ke amfani da Kuɗaɗen da Abacha ya sace

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, gwamnatin ta salwantar da wannan kudade wajen shiryen-shiryen ta na agaji da bayar da tallafi ta hanyoyin da suka dace.

A halin yanzu akwai kimanin daliban makarantu miliyan 8.5 na kasar nan dake amfanuwa da wannan kudade ta hanyar shirin gwamnatin tarayya na ciyarwa kamar yadda Ministan ya bayyana.

KARANTA KUMA: Zan goyi Bayan duk Amintaccen 'Dan Takarar Gwamna daga Mazabar Jihar Ogun ta Yamma - Obasanjo

Kazalika gwamnatin tarayya na amfanar matasan kasar nan ta hanya mashahurin shirin nan na N-Power baya ga jari da take baiwa mata 200, 000 da masu sana'ar hannu domin gudanar da harkokin su na kasuwanci.

Ministan ya kara da cewa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana nan tayi tsayuwar daka domin tabbatar da adalci gami da gaskiya wajen gudanar da dukiyar al'ummar kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel