Gwamna Bindow ya nada sababbin Kwamishinoni 2 a Gwamnatin sa

Gwamna Bindow ya nada sababbin Kwamishinoni 2 a Gwamnatin sa

Labari ya zo mana cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibrila ya canza wasu Kwamishonin sa da su ka sauya-sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta APC ya nada wasu sababbi.

Gwamna Bindow ya nada sababbin Kwamishinoni 2 a Gwamnatin sa

Gwamna Jibrila Bindow ya nada sababbin Kwamishinoni bayan wasu sun bar APC
Source: Depositphotos

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa Gwamna Bindow Jibrila ya sallami Kwamishinonin sa 2 da su ka bar Jam’iyyar APC su ka koma APC. Yanzu Gwamnan ya nada wasu Kwamishinonin da za su canji wadanda su ka sauya shekar.

Kwanakin baya ne Alhaji Yayaji Mijinyawa da Alhaji Umar Daware su ka fice daga Jam’iyyar APC zuwa PDP. Wadannan Bayin Allah ne ke rike da Ma’aikatar filaye da kuma Ma’aikatar kasuwanci da masana’antu na Jihar Adamawa.

KU KARANTA: Abin da kurum zai sa mu dawo bakin aiki a Majalisa

Yanzu dai Gwamnan ya nada wasu domin su maye guraben wadannan ‘Yan siyasa. Sababbin Kwamishinonin da aka nada su ne Usman Tukur daga Karamar Hukumar Fufore da kuma Iliyasu Bello wanda ya fito daga Yankin Yola.

Sababbin Kwamishinonin da aka nada sun yi alkawarin yi wa Gwamnan Jihar mubaya’a. Ba mamaki wadanda su ka bar Gwamnatin a baya dai sun yi haka ne domin komawa wajen tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Kwanaki kunji cewa Atiku Abubakar ya shirya wani taro a Garin Yola inda ya kaddamar da yakin neman zaben Shugaban kasa. A dalilin haka ne wasu manyan ‘Yan siyasan Jihar su ka bar APC su ka koma PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel