Yan kunar bakin wake 5 sun hallaka a harin da suka kai Maiduguri

Yan kunar bakin wake 5 sun hallaka a harin da suka kai Maiduguri

Yan kunar bakin waken kungiyar tada kayar bayan Boko Haram biyar sun hallaka kansu a wani mumunan harin da suka kai garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno ranan Lahadi, 5 g watan Agusta, 2018.

Jama'a na zaune kalau sai suka ji tashe-tashen Bam wanda ya tayar da msus da hankali kuma suka nemi mafaka.

Duk da cewa babu wani dan gari da ya rasa rayuwarsa sabanin yan kunar bakin waken biyar, wasu mazaunan Kaleri sun jikkata.

A jawabin da kakakin hukumar bada agaji na gaggawa wato National Emergency Management Agency (NEMA), shiyar arewa maso gabas, AbdulKadir Ibrahim, ya tabbatar da hakan.

KU KARANTA: Ba zan biyewa Mataimaki na ba – Gwamna Ganduje

Jawabin tace: "Bama-bamai sun tashi a harabar Maidiguri, unguwar Kaleri misalin karfe 9:53 na daren ranan Lahadi."

Wadanda abin nan ya shafa sune yan kunar bakin waken biyar da suka mutu, sannan wasu mutane uku da suka jikkata."

Duk da nasarar da hukumar sojin tarayya ke samu kan yan kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, yan ta'addan basu gushe sun kai hare-hare musamman na kunar bakin wake cikin gari ba.

A kwanakin baya, yan Boko Haram sun kai mumunan hari barikin soji inda suka hallaka wasu jami'an tsaro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel