Kusoshin Jam’iyyar APC sun fice daga Jam’iyyar a Jihar Kaduna

Kusoshin Jam’iyyar APC sun fice daga Jam’iyyar a Jihar Kaduna

Mun samu labari cewa a jiya Jam’iyyar adawa ta PDP tayi wani irin taro da sai dai iyaka ganin idon mutum. Wasu tsofaffin jiga-jigan Jam’iyyar APC ne su ka fice daga Jam’iyyar su ka dawo PDP.

Kusoshin Jam’iyyar APC sun fice daga Jam’iyyar a Jihar Kaduna

Sanata Hunkuyi wajen taron dawowa Jam’iyyar PDP. Hoto daga Daily Trust

Ana tunani kusan mutum sama da 200, 000 su ka halarci bikin wankan da aka yi sababbin shigowa Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna. Sanata Suleiman Othman Hunkuyi da kuma Mabiyan sa ne su ka sauya sheka inda su ka bar APC.

Bayan nan kuma akwai wani tsohon ‘Dan Majalisar dokoki da Tarayyar Jihar watau Hon. Isa Ashiru Kudan da ya tattara ya bar APC ya dawo Jam’iyyar PDP. Dama dai manyan ‘Yan siyasan sun bar PDP ne kafin zaben 2015.

KU KARANTA: Abin da ya sa Mataimakin Ganduje yayi murabus

Kusoshin Jam’iyyar APC sun fice daga Jam’iyyar a Jihar Kaduna

Wasu Magoya bayan Sanata Hunkuyi wajen taron da aka yi a Kaduna

Manyan ‘Yan siyasar sun bayyana cewa sun yi kuskure a zaben 2015 don haka su ka sha alwashin kifar da Gwamnatin Nasir El-Rufai. Manyan ‘Yan Jam’iyyar APC da dama dai yanzu sun bar Jam’iyyar sun komawa PDP a Kaduna.

Sanatan Kaduna ta Arewa Suleiman Othman Hunkuyi ya nemi Jama’a su tika APC da kasa a zabe mai zuwa saboda mawuyacin halin da su ka jefa al’ummar Kasar. Ba mamaki Sanata Suleiman Hunkuyi zai yo takarar Gwamna a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel