Siyasar Kano: Ba zan biyewa Mataimaki na ba – Gwamna Ganduje

Siyasar Kano: Ba zan biyewa Mataimaki na ba – Gwamna Ganduje

Mun samu labari cewa Mai Girma Gwaman Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano yayi na’am da murabus din da Mataimakin sa Farfesa Hafizu Abubakar yayi a karshen makon nan.

Siyasar Kano: Ba zan biyewa Mataimaki na ba – Gwamna Ganduje

Gwamna Ganduje ya amince da murabus din Mataimakin sa

Gwamna Abdullahi ya aikawa tsohon Mataimakin Gwamnan na Kano takarda inda ya amince da matakin da ya dauka na barin ofis. Gwamnan ya maida martani game da wasu batutuwa da Mataimakin na sa ya fada a wasikar sa.

Mai Girma Gwamnan na Kano ya nuna cewa bai da niyyar biyewa Mataimakin na sa ayi ta ce-ce-ku-ce, amma Ganduje ya bayyana cewa abin da Farfesa Hafiz Abubakar ya fada ba gaskiya bane domin kuwa ya ba sa damar yin aikin sa.

KU KARANTA: Wasu manyan Hadiman Gwamnan Kano Ganduje 3 sun ajiye aiki

Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai lokutan da Mataimakin ne ma ya rike ofishin sa a lokacin da ba ya nan, Gwamna Ganduje yace ko da ya dawo ofis bai sake matakan da Mataimakin na sa na wancan lokaci ya dauka ba.

Gwamnan dai yayi wa Mataimakin na sa addu’ar Allah ya ba sa sa’a wajen aikin sa inda zai koma jami’a inda ya fi wayau. Dama kafin nan kun ji dalilin da ya sa Hafiz Abubakar din ya ajiye aikin na sa bayan shekaru fiye da 3 a Gwamnati.

Jiya kun ji cewa siyasar Kano tana ta cigaba da sauya zani bayan wasu manya a Gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje sun yi murabus. Wasu manyan Hadiman Gwamnan na Kano kusan 4 ne su ka ajiye aiki a cikin ‘yan kwanakin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel