Dalilin da yasa ba zamu janye hutun da muka tafi ba – Mambobin majalisar wakilai

Dalilin da yasa ba zamu janye hutun da muka tafi ba – Mambobin majalisar wakilai

Wata kungiyar ‘yan majalisar wakilai (PDG) ta bayyana cewar ba zasu janye hutun da suka tafi ba matukar ana bukatar su dawo ne don a canja shugabancin majalisun tarayya.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar yau a Abuja ta hannun kakakinta, Honarabul Timothy Golu, ta bayyana cewar duk da shugabannin majalisar sun hadu domin tattauna yiwuwar dawowarsu bayan fadar shugaban kasa ta roke su, ‘yan majalisar sun bayyana cewar sai an yi masu alkawarun cewar ba za a taso da maganar canja shugabancin majalisun ba idan suka dawo.

Shugabannin mu na majalisa sun hadu domin tattauna yiwuwar janye hutun da muka tafi kamar yadda fadar shugaban kasa ta nema. Dole mu samu tabbacin cewar ba za a yi wani yunkurin taka doka ta hanyar bijiro da batun canja shugabancin majalisun ba.

Dalilin da yasa ba zamu janye hutun da muka tafi ba – Mambobin majalisar wakilai

Zauren majalisar wakilai

Mun damu matuka da kalaman wasu ‘yan majalisa dake adawa da Saraki kamar su Sanata Abdullahi Adamu da Ali Ndume na cewar sai ya ajiye mukaminsa na shugaban majalisar dattijai.

DUBA WANNAN: Tsige Bukola: An yi ganawar sirri tsakanin Osinbajo da shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai

“Muna son zaman lafiya da kuma ‘yancin dimokradiyya kuma zamu bijirewa duk wani yunkuri na son ganin an tursasa mu yin duk wani abu da ya saba doka.” A cewar sanarwar.

‘Yan majalisar sun bayyana cewar bai kamata bangaren zartarwa ya ke tsoma baki a cikin harkokin majalisun kasa ba, yin hakan sabawa dokokin mulkin kasa ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel